Me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, da makaman Gwamnati ‘yan Bindiga ke amfani suna kai hare-hare a kasarnan.
Ya bayyana hakane a wajan taron lalata muggan makamai da suka yi yawa a tsakanin mutane.
Yace yawanci makaman na zuwa hannun ‘yan Bindigar ne daga wajan bata garin jami’an tsaro.
Yace gwamnati zata yi dukkan mai yiyuwa dan magance wannan matsalar.