Monday, December 16
Shadow

Yadda ake fanke mai dadi

YADDA AKE FANKE

  • Bota
  • Kwai
  • Madarar fulawa
  • Fulawa
  • Sukari
  • Bakar hoda/ Yeast
  • Gishiri kadan
  • Filebo

HADAWA:
A samu fulawa a tankade ta sannan a jika sukari a dama da ruwa kadan a kofi a yi ta gaurayawa har sai ya narke. A zuba fulawa a kwano, a zuba bota kamar cokali 2, a dirza ta da fulawa har sai ta bata a cikin fulawa. Sannan a zuba yeast kamar cokalin shan shayi biyu a ruwan dumi a jira na kamar minti 5, bayan minti 5 za a ga ya dan yi kumfa a saman kofin.

Sannan a zuba madarar fulawa da gishiri rubu’in cokalin shan shayi da filebo, a fasa kwai kamar biyu. Sannan a ci gaba da murzawa. A zuba ruwan yeast a kwaba sannan, a dauko ruwan sukarin nan a zuba ana kwabawa har sai yadan yi kauri haka daidai kwabin fanke. Bayan sun kwabu sosai. Sai a rufe na tsawon yini guda. Wadansu kuma za su iya jiransa sai ya tashi kafin tuya.

Karanta Wannan  Yadda ake dafa ganda

Bayan kwabin ya tashi, sai a dora man gyada a tukunyar tuya a yanka albasa. Bayan ya yi zafi sai a rika yankawa daidai girman fanken da ake so. Har sai sun toyu sannan a kwashe a sanya wa maigida a kwanon karyawarsa.

Za a iya cin wannan fanken da shayi kuma ya fi dacewa da karyawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *