Monday, December 16
Shadow

Yadda ake zobo mai dadi

YADDA AKE ZOBO DRINK

Abubuwan buqata

Sobo/zobo
Cucumber
Bawon abarba
Danyar citta
Kanumfari
Flavor
Sugar
Bevi mix cola da Bevi mix mango
Kamshi (Wanda ake samu a cikin kayan yaji amma optional ne)
Sai barkono kadan (optional)

Da farko za a tsince dim dattin da ke cikin zobo sai a zuba a tukunya babba a markada cucumber a wanke bawon abarba dik azuba akai,a zuba barkono kadan da kamshin kayan yaji (optionals ne) a zuba kanumfari da jajjagaggiyar citta akai sai a zuba ruwa a Dora kan wuta ya tafasa sosai a tace a kara ruwa akai a sake tacewa har sai zobon ya salamce sai a ajiye domin ya rage zafi sai a zuba sugar,flavor na ruwa,da kuma Bevi mix (wadanda ba sa so wannan zasu iya Saka iya sugar kawai) sai juya su su hade jikinsu sosai a kara tacewa sai a juye a jug or a kulla a Leda ko a robobi/gorina a zuba a fridge yayi sanyi ko a saka masa kankara yayi sanyi , shikenan an kammala wannan kalan zobon sai Sha…

Karanta Wannan  Yadda ake dafa kazar amarya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *