Wednesday, January 15
Shadow

Hadin man gyaran fata

Asamu

  • ganyan magarya
  • man zaitun
  • man habbatussauda
    Ana daka ganyan magarya a zuba cikin man zaitun da man habbatussauda
    Anasha shafawa sau 2 a rana shi ma yana gyaran
    Jiki yana kashe cututtukan fata
    Insha allah.

Sabulun gyaran fata,salaushinta dakuma maganin tabo

Kisamu sabulun salo,wato ghana soap,kisami madara,leman tsami dakuma kurkur da haska amarya,kisamu sabulun broonze bashida tsada ana saidashi a stores haka saikuyi kokari kunemi sabulun caramel shima duk acikin kayan hadine to kisamu kihada sabulun duka ki daddakasu kokuma ki yanyankasu siri siri saiki gwamutsasu sannan saikikawo kurkur daidai misali ki juye kisamu haska amarya daidai misali shima ki juye.
haska amarya da kurkur agidagen gyaran jiki ake samunshi saikihadeshi asabulun kibuge sannan wasu sunasa nescafe domin yanasan laushin fata inkinaso kisaka inbakyaso saiki barshi saikijuye madararki ki buga saikikawo ruwan leman tsaminki dakika matse shima ki juye,idan kikai hakan saiki bugesu sosai su hade,zakiga yayi ruwa ruwa amman ba komai bane,saiki juye wannan hadin cikin container mai murfi ki rinka wanka dashi wannan hadin yanamugun gyara fata,ba bleaching yakeyiba,gyarafata yake yanakuma maganin kujaren fata dakuma kurajen fuska yana mugun gyaran jiki sosai kuma yanada kyau ku rinka shafa sabulunnan kamar anasaura awa daya kiyi wanka yanadakyauma kisamu ganyen magariya busasshe ki daka kizuba akan sabulun dakika hada kikara bugewa bakaramin kyau zakiba duk tabon dake jikinki saikinnema kinrasasu mata ayi kokari agyara fata dan miji yakalla yaji dadi yanasa santsin fata dakuma laushinta.

Karanta Wannan  Gyaran fuska da man zaitun

Gyaran Fata

zaki tanadi ababe
kamar haka:

  1. Man Zaitun
  2. Lalle
  3. Kur-kur
  4. Madarar ruwa (peak)
    Za ku hade wadannan kayan hadin guri guda sai ku kwaba su ku shafe jikinku da fuskar ku, za ku yi wannan hadin kafin ku shiga wanka idan ya bushe a jikin ku sai ku murje sannan sai ku shiga wanka,
    wannan hadin ya na sa jiki yayi kyau da sheki insha Allahu.
    Za ku iyayin wannan ma wanda ake hada:
  5. Kur-kur
  6. Dilka
  7. Zuma kwai
  8. Lemon tsami
    Za ku hade su a guri guda ku samu ruwan
    ku kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma ya fi kwabin lallen ruwa, sai ku shafe fuskanku, idan kuma har da jiki kuke so, sai ku shafa harada jiki bayan awa daya sai ku shiga wanka za k ga yadda jikinku
    zai goge. Das da izinin Allah.
Karanta Wannan  Hasken fata cikin kankanin lokaci

Idan kuma gyaran fuska ku ke so sai ku
tanadi:

  1. Dettol
  2. Sabulun Ghana
  3. Garin Zogale
  4. Farar albasa.
    Sai ku hade su guri guda ku kurba su a turin ku mulmula ku rinka wanke fusku za ku ga yadda fuskarku za ta y i kyau.
    Wannan kuma hadin yanasa fuska ya yi haske ya yi kyau da annuri ya kuma kore kurajen fuska za’a tanadi abae kamar
    haka: Bawon kankana sai a runka goge guska da shi yana gyara fuska ya yi sumul.

Ga kuma wani hadin duk na gyaran fatar jiki shi ma wannan hadi ne na musamman wanda ya ke sa fatar mace ta zamo tana tare da shauki da laushi kai har ma zaki ji jikin ki yana wani damshi damshi wannan hadi ne da yawanci amare ka wai ake yi
wa shi.
Za ku tanadi ababen kamar haka:

  1. Ayaba
  2. Lemon tsami
  3. Tataciyar madara
  4. Kwai daya
    Za ku sami ayaba mai kyau ku bare ki matse da hannuku, ko ku markada a
    blenda ya yi laushi, sai ku zuba tataciyar madara ku fasa kwai kamar guda daya amma farin zaku zuba sai ku matse lemoun tsami ku gauraye shi ku shafa a jikin ku ya samu kamar tsayin awa daya, sai uk yi wanka da ruwan zafi, idan har
    kuka lazinci yin haka kamar kwana uku za
    ku sha mamaki.
Karanta Wannan  Maganin kurajen fuska

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *