Kamfanin TCN ya bayyana ranar Lahadi, 3 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da zai gyara wutar lantarkin Arewa.
Kamfanin yace yana yin dukkan mai yiyuwa dan ganin ya dawo da wutar zuwa yankin Arewa.
Wakilin Kamfanin, Sule Abdulaziz ne ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a babban birnin tarayya, Abuja ranar Talata.
Tun ranar 22 ga watan October ne dai aka fara samun matsalar wutar.
Ya kara da cewa suna kokarin dawo da wutar ne bisa kokarin basu tsaro da sojojin Najeriya ke yi.