
Mahaifin me kudin Duniya, Elon Musk watau Errol Musk ya kare dansa bayan da aka tambayi ra’ayinsa game da da na 13 da dansa ya haifa da wata shahararriyar me amfani da kafafen sadarwa me suna Ashley St. Clair.
Mahaifin na Elon Musk yace ai mahaukaciya ce kawai ba zata amincewa dansa ya dirka mata cikin shege ba.
Elon musk dai yana da jimullar ‘ya’yaye 14 wanda ya haifa tare da mata 4.
Shima dai mahaifin na Elon Musk, Errol ‘ya’yansa 7 2 daga cikinsu ya haifesu ne tare da diyar matarsa, watau Agola.