Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC ta yo gargadin daina amfani da wani kalar Turaren Nivea Roll-on saboda illar da yake dauke da ita.
Kalar turaren da ta ja kunne kan amfani dashi shine Nivea Black & White Invisible Roll-on deodorant saboda yana dauke da wani sinadari da aka haramta amfani dashi a cikin turaruka.
Tuni kungiyar Kasashen Turai ta EU ta fitar da sanarwa akan daina amfani da wannan turare inda tace duk ma wadanda suka sayeshi su mayar dashi ga kamfanin.
Shi wannan sinadari dai na taba lafiyar haihuwar masu amfani dashi inda yawan amfani dashi na iya kai ga mutum ya kasa haihuwa sannan yana taba lafiyar yaron da ba’a haifa ba idan mace me ciki na amfani dashi sannan kuma yana sanya kaikai a jikin mutum.
Shi wannan sinadari dai sunansa 2-(4-tert-Butylbenzyl propionaldehyde (BMHCA).
Dan haka hukumar ta ja hankalin masu shigo da wannan turare daga kasar waje da masu sayensa su kula kada su rika fani da wannan kalar Turaren na Nivea.