Thursday, December 26
Shadow

Ko kunsan cewa kotu tace a ci gaba da tsare yaran da gwamnati ke zargi da cin amanar kasa sai ranar 1 ga watan Janairun 2025 sannan za’a ci gaba da shari’ar su?

Babbar Kotun tarayya dake Abuja inda aka gurfanar da yaran da gwamnati ke zargi da cin amanar kasa ta bayar da umarnin a kaisu gidan yari a ci gaba da tsaresu har sai ranar 1 ga watan Janairun 2025 sannan a ci gaba da shari’a.

Saidai a wani sabin rahoto da hutudole ya samu, babban lauyan Gwamnati ya bukaci a mayar da maganar shari’ar yaran ofishinsa inda kuma ya nemi a dawo da ranar ci gaba da shari’ar kusa.

A wata majiya daga ma’aikatar shari’ar tace ana tsammanin nan da ranar Talata me zuwa za’a iya dawowa a ci gaba da shari’ar sannan kuma gwamnati na shirin janye zargin da takewa yaran.

Karanta Wannan  Hotuna: 'Yan Bindiga sun kashe babban soja da bai dade da yin aure ba da sauran sojoji 3 a Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *