Wani sautin muryar Rahoton BBC ya bayyana da ya ruwaito kakakin ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa na cewa sun kama mutane 76 sun kaisu Abuja saboda cin amanar kasa ta hanyar daga tutar kasar Rasha yayin zanga-zangar yunwa.
Idan dai ba’a manta ba, jimullar mutanen da aka kai kotu ranar Juma’ar data gabata 76 wanda daga cikinsu 32 kananan yara ne.
Hakanan a cikin Rahoton na BBCHausa an ji muryar kwamishinan Shari’a na jihar Kano yana tabbatar da cewa suna sane da kama wadannan yara.
Lamarin gurfanar da wadannan yara a gaban kotu dai ya dauki hankula a ciki da wajen Najeriya inda akaita Allah wadai.
Zuwa yanzu dai Babban Lauyan gwamnati ya karbi maganar shari’ar yaran kuma ana tsammanin gwamnati zata yafe musu laifin cin amanar kasa da ake zarginsu dashi.