Wannan mutumin wanda dan kasuwane dan kasar Equatorial Guinea ya shiga idon duniya bayan da bidiyo sama da guda 400 suka bayyana inda suka nunashi yana lalata da mata.
Wani abin karin ban mamakin shine cikin matan da yayi lalata dasu hadda matan aure da kuma matan manyan ‘yansiyasa na kasar.
Rahotanni sun ce cikin matan manyan mutanen da yayi lalata dasu akwai matar ministan shari’a na kasar, da matan sauran ministoci.
Akwai kuma matar kaninsa.
Da matar kawunsa.
Da matar Faston cocin da yake halarta.
Da matar uban gidansa.
Da matar me tsaron lafiyarsa.
Da abokan kanwarsa da dai sauransu.
Rahoton yace mutumin baya amfani da kwandam wajan yin lalata da matan.
Tuni dai an garzaya dashi kotu inda kotun tace a je a gwadashi ko yana dauke da cutar dake yaduwa ta wajan jima’i kamar su ciwon sanyi da kanjamau.
Mutumin bidiyon da kuma tsiraicin dake ciki yasa shafin hutudole ba zai iya wallafa musu su ku kalla ba.
Saidai muce Allah ya kyauta.