Monday, December 9
Shadow

Farashin kayan Abinci zasu tashi a Najeriya saboda babu Network a bankuna

Matsalar rashin Network a bankunan Najeriya yasa ake tsammanin samun hauhawar farashin kayan abinci.

Manyan jiragen ruwa sun kawo abunci kala-kala daga kasashen waje inda suke gabar tekun Legas suna jira a kammala duk takardunsu na haraji wadanda suka makale a bankuna saboda matsalar rashin Network.

Rahoton daga jaridar Naigerian Tribune yace kayan auna kan ruwa inda masu kayan suke jiran takardunsu, inda matsalar take shine duk kwana daya da kayan suka kara sai mai kaya ya sake biyan kudin haya na Kwantena da kayansa suke ciki.

Wakilin masu kawo kayan Mr. Frank Ogunojemite ya bayyana cewa, suna bukatar gwamnati ta rika basu wani dauki ko tallafi a irin wannan yanayi saboda ba laifinsu bane.

Karanta Wannan  Naira ta karye a Kasuwar Chanji: Farashin dala a yau

Yace duka kudin hayar da suka biyawa kayan nasu akan wanda zasu sayi kayan zasu fanshe dan haka dole ne kayan masarufi su rika yin tsada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *