Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin sakin dukkan ƙananan yaran da aka kama da zargin cin amanar ƙasa sakamakon shiga zanga-zanga kan tsadar rayuwa.
Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce an kuma kafa wani kwamati da zai bincika yadda aka kama su da sauran lamurransu.
“Shugaban ƙasa ya ce a sake su kuma a sadar da su ga iyayensu,” in ji ministan lokacin da yake magana manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Bayanan sun fito ne jim kaɗan bayan kammala rantsar da sababbin ministoci bakwai da Shugaba Tinubu ya naɗa a fadarsa a yau Litinin.
Kwamatin da zai yi aikin zai kasance ƙarƙshin ma’aikatar agaji da rage talauci, in ji ministan.