Rahotanni daga jihar Sokoto na cewa wata sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda ta bulla a jihar.
Mataimakin gwamnan jihar, Idris Gobir ne ya bayyana haka a yayin ziyarar da wata tawagar rundunar tsaro ta kasa ta kai masa ziyara.
Yace sunan wannan sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda, LAKURAWAS kuma kungiyace dake danganta kanta da addini.
Sannan ya kara da cewa sun fara gudanar da ayyukan ta’addanci a wasu garuruwan na jihar Sokoto.
Sannan kuma yace kungiyar ta mallaki muggan makamai.
Hakan na zuwane yayin da jihar ta Sokoto ke fama da matsalar hare-haren ‘yan Bindiga wanda mataimakin gwamnan yace jami’an tsaro na aiki tukuru dan magancewa.