A sunnah ta ma’aiki, Sallallahu Alaihi Wasallam babu wata addu’a da aka ruwaito cewa itace ta janyo hankalin saurayi.
Saidai zaki iya rokon Allah ya baki soyayyar wane, idan shine Alkhairi.
Kuma mafi kyawun hanyar da ya kamata ki bi wajan yin wannan addu’a shine ta hanyar yin Istikhara.
Jabir ibn ‘Abd-Allah(RA) ya ruwaito cewa, Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam yana koya mana neman zabin Allah(yin Istikhara) kamar a dukkan al’amuran mu, kamar yanda ake koya mana karatun Qur’ani.
Yace duk wanda yake da wata damuwa akan wani abu da yake nema ko yake so to yayi raka’a biyu sai yace “Allahumma inni astakhiruka bi ‘ilmik, wa astaqdiruka bi qudratik, wa asaluka min fadlik al-azim. Fa innaka taqdiru wa la aqdir, wa ta’lamu wa la a’lam, wa anta ‘allamul-ghuyub. Allahumma in kunta ta’lam anna [hadhal-amr] khayrun li fi dini wa ma’ashi wa ‘aqibati amri, faqdurhu li, wa yassirhu li, thumma barik li fih. Wa in kunta ta’lam anna [hadhal-amr] sharrun li fi dini wa ma’ashi wa ‘aqibati amri, fasrifhu ‘anni wasrifni ‘anhu waqdur li al-khayr haythu kan. Thumma ardini bih”
Bukhari, 1109.
Allah ne mafi sani.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole