Friday, December 6
Shadow

Alamomin mace tana son saurayi

Alamomin mace tana son saurayi suna da yawa, kuma a wannan rubutu, zamu yi kokarin kawo muku su kamar haka:

Da kanta zata rika gaya maka tana sonka: Ba kasafai ake samun irin wannan ba, idan mace na sonka da gaske, zata rika gaya maka tana sonka, kuma zata rika gaya maka hakanne cikin shauki da shagwaba da nuna kaguwa.

Ba ta son rabuwa da kai: Macen dake son saurayinta, a duk sanda suka hadu zaka ganta tana yin kamar ta hadiyeshi, bata son yayi Nesa da ita, tana yawan murmushi, sannan idan zasu rabu, bata jin dadin hakan.

Yawan Kallo: Macen dake son saurayinta sosai, bata gajiya da kallonsa, idan suka hadu zata yi ta kallonshi, idan kuma basa tare, zata yi ta tambayar yaushe zai je tadi, sannan zata yi ta Neman ya tura mata hotunansa.

Karanta Wannan  Maganin farin jinin samari

Zata rika damuwa dashi: Idan mace tana sonka zata rika damuwa da kai sosai, zata yawaita kiranka a waya, zata rika tambayarka ya aiki ko sana’arka, zata rika tambayar yanayinka, zata rika tambayarka ‘yan gidanku da sauransu.

Zata yi maka kyauta: A bisa al’ada, Namiji ne aka fi ganin yawa mace kyauta, amma idan soyayya ta kai kololuwa, mace ma tana yiwa namiji kyauta.

Zata rika baka shawarar inganta rayuwarka: Idan mace ta kasance tana son saurayi, zata rika bashi shawara akan yanda zai kyautata rayuwarsa, idan taga yayi wani Abu da bai dace dashi ba, zata bashi shawarar ya gyara.

Zata rika tambayar yaushe zasu yi aure: Idan mace na son saurayi, zata rika kaguwa, tana tambayar yaushe zasu yi aure, tana Neman ya turo a saka musu rana.

Karanta Wannan  Yadda ake ma saurayi shagwaba

Zata rika yi maka kwalliya: Idan mace na sonka da gaske, a duk sanda zaku hadu, da wuya ka ganta da kazata, zata rika so yin kwalliya Dan ta burgeka.

Zata rika jin nauyin Kiran sunanka: Idan mace na sonka da gaske, zata rika jin nauyin Kiran sunanka kai tsaye, sai dai tace maka baby, ko masoyi ko sweet heart da dai sauransu.

Zata rika kiranka da sunan babban danku na farko: Watakila zaku iya yin fatan samun da namiji a matsayin danku na farko, kuma har ma Ku saka masa suna, misali Walid, to budurwarka zata iya rika kiranka da sunan Baban Walid.

Karanta Wannan  Yanda mace zata yi kukan shagwaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *