A ranar Litinin an sayo dalar Amurka akan Naira 1,725.
Hakan na nuna cewa Nairar ta samu daraja idan aka kwatanta da farashin da aka sayi dalar a ranar Juma’a data gabata watau Naira 1,735.
Wannan farashi na kasuwar bayan fage ce.
Amma a farashin Gwamnati, Naira faduwa ta yi inda aka sayi dala akan Naira 1,676.