Shugaban jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri inda yace su ci gaba da baiwa gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri.
Yace matsalolin da ake fama dasu, Tinubu ya gajesu ne daga Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ganduje ya bayyana hakane a wajan taron kaddamar da wani Littafi kan cika shekara 1 da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi akan mulki.
Ganduje ya kara da cewa, matakaj da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yake dauka na kawo gyara aun fara nuna alamar nasara.