Kamfanonin rarraba wutar Lantarki na Najeriya, Discos sun kara farashin mitar wutar lantarki.
Wannan ne karo na biyu da suka kara kudin wutar a cikin watanni 4 da suka gabata.
Discos sun ce mita me layi daya ta tashi daga farashin kusa da 117,000 zuwa 149,800.
A watan Augusta da ya gabata ne dai aka samu karin farashin mitar wutar lantarkin na karshe.