‘Yansanda a jihar Imo sun tabbatar da mutuwar mutane 2 bayan da bam ya fashe a kasuwar Orlu ranar Talata.
Kakakin ‘yansandan jihar, ASP Henry Okoye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a babban birnin jihar,Owerri.
Yace mutane da yawa dake gudun neman tsira sun jikkata a harin inda yace suna kan bincike akan lamarin.
Yace Wadanda suka mutu din wanda suka je saka bam dinne inda kamin su kammala sakashi ya tashi dasu.
Kwamishinan ‘Yansandan jihar, CP Aboki Danjuma ya aika da jami’an ‘yansanda na musamman dake da kwarewa akan harkar bam wajan.