Amurkawa da yawa sun kwana da bakin ciki bayan da Donald Trump ya sake cin zabe a kasar a karo na biyu.
Bidiyo da yawa sun bayyana inda suke nuna yanda Amurkawan ke takaici da mamakin cewa wai Donald ne ya sake cin zabe.
Wasu an gansu suna kuka wasu suna takaici, wasu ma basu san abinda zasu yi ba.
A hannu daya kuma wasu fitowa suka yi akan tituna suna zanga-zangar kin amincewa da shugabancin Donald Trump inda suke cewa Donald Trump must go.
An samu irin wannan zanga-zanga a biranen Chicago, Philadelphia, da New York city.
Donald dai na da tsare-tsare irin na Kiristanci inda bai yadda a zubar da ciki ba, bai yadda da ‘yan madigo da luwadi ba bai yadda a rika canja jinsi ba, watau Namiji ya je a masa aiki ya koma mace ko mace ta je a mata aiki ta koma Namiji.
Hakanan Donald Trump baya son baki ‘yan cirani, hakanan baya son yake-yake.
Saidai a bangare guda kuwa ita Kamala Harris tana so ko bari a yi kusan duka abinda muka bayyana a sama.
Wannan ne yasa wasu ke son Donald Trump musamman asalin Turawa Amurkawa dake da akidar gyara kasa da kuma hana lalata tarbiyya.
Inda a bangare daya kuma masu son a bari a yi rayuwar ‘yanci, mutum yayi abinda yake so, a sheke aya suke son Kamala Harris.