An kori mutumin da ake zargi da keta haddin matan aure kusan 400 a kasar Equatorial Guinea daga aiki
Shugaban kasar Equatorial Guinea Obiang Nguema Mbasogo, ya sanar da korar Baltasar Ebang Engonga daga shugabancin hukumar kula da binciken kudi ta kasar biyo bayan zargin fitar wasu faya-fayan bidiyo na keta haddin wasu matan manyan mutane a kasar.
Shugaban kasar ya sanar da nada Zenón Obiang Obiang Avomo a matsayin sabon shugaban hukumar bayan sallamar Baltasar.