Jakadan kasar Israela a Najeriya, Michael Freeman ya bayyana cewa, ba a gabas ta tsakiya ba kadai ayyukan ashsha na kasar Iran suka tsaya ba.
Yace ayyukan na kasar Iran sun shigo yankin Africa musamman Najeriya.
Ya kara da cewa, kasar ta Iran ce ke son ta tarwatsa Najeriya.
Ya bayyana hakane ranar Talata a Abuja wajan hada rahoton cikar harin da kungiyar HAMAS ta kauwa kasar ta Israela na October 7.
Mutane 396 ne dai kungiyar ta Hamas ta yi garkuwa dasu bayan hare-haren da suka kai inda daga baya suka saki wasu daga ciki bayan shiga tsakani da kasar Amurka da Majalisar dinkin Duniya suka yi.
Saidai har yanzu akwai mutane 101 a hannun kungiyar ta Israela.
Freeman ya bayyana kasar Iran a matsayin shedaniyar kasa wadda yace tana amfani da karnukan farautarta irin su Hamas da Hezbollah wajan jefa dubban mutane cikin halin kaka nikayi, yace Najeriya ma bata tsira daga sharrin na kasar Iran din ba.
Ya bayyana cewa kasarsa zata daina yaki a Lebanon ne kawai idan ya zamana an aiwatar da tsarin majalisar dinkin Duniya daya ce Hezbollah ta ajiye makamanta.
Ya kara da cewa a yanzu suna yaki da kasashe 7 wanda kuma duka kasar Iran ce ke daukar nauyin su.