Monday, December 16
Shadow

An samu lauyan da zai kare mutumin da ya cinna wa masallaci wuta a Kano

Babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zama a Kano ta ɗage sauraron ƙarar da take yi kan wani matashi da ya cinna wa masallaci wuta a jihar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da jikkatar wasu.

A ranar 15 ga watan Mayu ne mutumin da ake zargi a watsa fetur tare da cinna wa masallaci wuta sa’ilin da ake sallar Asuba a ƙaramar hukumar Gezawa ta jiharn Kano.

Ya zuwa yanzu lamarin ya haifar da asarar ran mutum 19, yayin da wasu ke ci gaba da samun kulawa a asibiti.

A lokacin zaman kotun na yau, alƙali ya bayyana cewa an samu lauyan da zai kare wanda ake zargi, inda ya buƙaci a tattara duk wasu bayanai da hujjoji da suka kamata domin miƙa wa lauyan.

Karanta Wannan  Da Duminsa: 'Yansanda sun haramta hawan Sallah a Kano

Kotun ta ɗage shari’ar ne zuwa ranar huɗu ga watan Yulin 2024.

A zaman da kotun ta yi na farko, mutumin ɗan shekara 38 ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi a lokacin da kotu ta karanto masa su.

Kimanin mutum 40 ne aka yi ƙiyasin suna cikin masallacin a lokacin da lamarin ya faru.

Rudunar ƴansandan Najeriya a jihar Kano ta ce binciken da ta yi na farko-farko sun tabbatar mata cewa wanda ake zargin ya kai hari a masallacin ne sanadiyyar rikici game da rabon gado.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *