Rahotanni sun nuna cewa,gwamnan jihar Edo me barin Gado Godwin Obaseki ya tsere daga jiharsa saboda tsoron kamun EFCC.
Gwamna me jiran gado, Senator Monday Okpebholo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta bakin kakakinsa, Godspower Inegbe.
Yace Gwamna Obaseki yayi amfani da motar bas ne yayi basaja ya tsere daga jihar.
Yace ikirarin gwamnan na cewa shi me mutanene karyace inda ba haka ba bai kamata yayi amfani da bas ys tsere daga jihar ba.
A baya dai an ji gwamna Obaseki na fadin cewa yasan hukumar yaki da rashawa da cin hanci EFCC na shirin kamashi bayan ya sauka daga kan mulki amma baya jin tsoro.