Kamfanin Man fetur na kasa,NNPCL ya dakatar da sayo man fetur daga kasar waje inda ya amince ya sayi man fetur din daga wajan Matatar man fetur din Dangote da sauran matatun man fetur masu zaman kansu.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari ya bayyana haka a wajan wani taro da ya faru a Legas ranar Litinin.
Hakan na zuwane yayin da ‘yan kasuwar man fetur suka nace saidai su sayo man fetur din daga kasar waje maimakon sayowa daga hannun matatar man Dangote saboda a cewarsu,man fetur din da suke kawowa daga wajen ya fi na Dangote sauki.
Kyari ya kuma musanta cewa suna yiwa matatar man fetur ta Dangote zagon kasa inda yace suma suna da hannun jari a matatar.