Hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta kasa, EFCC ta gayyaci wani dan kasar Nijar me suna Ibrahim Mohammad saboda yanda aka yi liken kudi a wajan bikinsa.
Hakan ya biyo bayan watsuwar Bidiyon bikin a kafafen sada zumunta inda aka rika kiran EFCC da ta dauki mataki akan lamarin.
Kakakin hukumar, Dele Oyewale ya fitar da sanarwa akan lamarin inda yace da farko an danganta bikin da diyar Danjuma Goje me suna Fauziyya amma daga baya da aka yi bincike an gano bikin na Hajara Seidu Haruna ne wadda ke harkar GwalaGwalai a Kano, Abuja da Dubai.
Yace wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.