Monday, December 16
Shadow

Meke kawo kaikayin dubura

Abubuwan dake kawo kaikayin dubura suna da yawa, ga kadan daga cikinsu kamar haka:

A wasu lokutan cutar da ta taba fatar mutum na iya sawa duburarsa ta rika kaikai ko kuma bushewar wajan musamman lokacin san yi zai iya kawo hakan.

Hakanan amfani da sabulu me kanshi ko hoda, ko wani kalar man shafawa a dubura ko gogeta da tsimma ko toilet paper duka na iya sawa ta yi kaikai.

Infection irin wanda ake dauka daga wajan jima’i, ko kuma irin wanda yake kama gaban mata, wanda ake cewa ciwon sanyi duk na iya sa dubura kaikai.

Basir wanda ke sa dubura ta kumbura ko ta rika fitar da jini ko ta rika zafi duk yana kawo kaikayin dubura.

Karanta Wannan  Maganin kaikayin dubura

Kalar abincin da ake ci irin su cakulan, Tumatir, abinci me yaji, giya, Kofi da sauransu duk suna sanya dubura ta rika kaikai.

Yanayin yanda ake tsaftace jiki bayan yin bayan gida shima yana iya sawa dubura ta rika kaikai.

Akwai wasu cutuka da suka hada da ciwon sugar da sauransu dake sanya dubura ta rika kaikai.

Shan wasu magunguna irin su Antibiotics, da Laxatives dake sa mutum yayi zawo na iya kawo kaikayin dubura.

Hakanan akwai wasu kananan tsutsotsi dakan yi yawo a duburar mutum wanda sukan sa mutum ya rika jin kaikai a duburarsa, wannan yawanci yafi faruwa da yara.

Karanta Wannan  Maganin kaikayin dubura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *