Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da kawo ƙarshen ƙungiyar ‘yan ta’adda da ake kira ‘Lukarawa’ a shiyyar Arewa maso yammacin nan ba da jimawa ba.
Ribadu ya bayyana haka ne a lokacin da ya wakilci shugaban kasa Tinubu a wajen bikin buɗe babban taron kwastam na shekarar 2024, ranar Laraba, a Abuja.
“Za mu fatattaki waɗanda ake kira Lukarawa daga kasarmu. Za mu kunyata masu sukar mu kuma zamu rufe bakunansu.
“Boko Haram da suka addabi kasarmu a baya, yanzu tserewa suke yi. Yanzu haka mambobinta suna tafiya zuwa wasu ƙasashe makwabta saboda ba su da damar yin ta’addancinsu a Najeriya” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa, alamun na ƙara nuna cewa al’amura na cigaba da inganta ta fuskar tattalin arziki a ƙasar nan wanda kowa zai iya gani, inda ya ba da misali da yadda ake hako danyen mai a yankin Neja-Delta da kuma sauye-sauyen kasafin kudi da babban bankin Najeriya (CBN) ke yi a cikin irin wannan kokari.
“Haƙar danyen mai ya kai ganga miliyan 1.8 a kowacce rana. sannan kuma an tsaftace babban bankin kasa, babu wanda ke ɗaukar kobo daga babban bankin.
“Mun yi alƙawarin cewa za mu gyara kasar nan, kuma za mu yi hakan domin Shugaba Tinubu bai taɓa zama mutum mai gazawa ba,” inji Ribadu.