‘Yansanda a jihar Legas sun kama wani mahaifi me suna Olamide Fatumbi me kimanin shekaru 25 saboda dukan diyarsa me shekaru 3.
Mutumin na zaunene a Afeez Street, Akesan, Igando, Lagos State kuma an zargeshi da cutarwa ga diyar tasa.
Saidai ya musanta zarge-zargen da akw masa.
Mai Shari’a, Mrs E. Kubeinjeya bayar da belin wanda akw zargi akan Naira dubu dari(100,000) da kuma mutane 2 da zasu tsaya masa.
An dage sauraren karar sai nan da zuwa 25 ga watan Yuni.