Thursday, September 3
Shadow

Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin dala Miliyan 23.35 daga Kuwait dan ta yi maganin matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna

Gwamnatin tarayya ta ciwo bashin Dala Miliyan 23.35 dan magance matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar Kaduna.

Gwamnatin ta saka hannu ta karbo bashin a madadin gwamnatin jihar Kaduna wanda wannan na daga shirin ciwo bashin Dala Miliyan  $62.8m dan magance matsalar rashin zuwan yara makaranta a jihar.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar kudi ta tarayya, Mohammed Manga ya tabbatar da hakan inda yace za’a yi amfani da wannan kudi dan inganta karatun akalla yara 100,000.

Sannan za’a yi amfani da kudin wajan gyaran makarantu da sauran abubuwan da suka shafi harkar ilimi a jihar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Dansandan kasar Ghana na ta shan yabo bayan da ya taimakawa wani me mota da kudi kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *