Shi kyau kala biyune Dana zahiri Dana badini.
Kyan Zahiri shine Wanda ake gani da ido, watau fuska me kyau, dogon hanci, fari, da sauransu.
Mace me Kyan zahiri za’a iya ganinta fara, doguwa, me matsakaitan mazaunai da matsakaitan nonuwa me fararen idanu, da fararen hakora sannan ta iya wanka.
Saidai shi Kyan zahiri yana dusashewa musamman Idan girma ya fara kama mace, shiyasa ake son mace ta hada kyau biyu watau na zahiri dana badini.
A lokuta da dama, mace zata iya samun kyan badini amma bata dana zahiri, to idan so samune, mace ta hada duka biyun, amma idan ya zama mutum zaba zai yi tsakanin mace me kyan badini bata dana zahiri da kuma me kyan zahiri bata dana badini, to a shawarce mutum ya dauki mace me kyan badini bata dana zahiri yafi.
Shi kuma kyan badini, yawanci ba’a ganinsa sai mu’amala ta hada.
Kyan badini ya hada da:
Ilimi na addini dana boko.
Tarbiyya me kyau irin ta addini.
Hakuri.
Iya tarairaya.
Iya kalamai tausasa.
Girmama na gaba.
Tsafta.
Rashin kwadayi ko daidaitashi.
Iya soyayya.
Kawauci.
Ibada.
Duk macen data hada wadannan ko mafi yawa daga cikin wadannan halaye to za’a iya kiranta da me kyau badini.
Idan kuwa ta hada kyan badini dana zahiri to ta taki sa’a.