Sunday, January 5
Shadow

Ya ake yiwa saurayi fira

Fira ko hira da saurayi abune me dadi musamman idan kuna son juna, watau yana sonki, kema kina sonshi.

Saidai ga budurwa da bata sababa, zata so sanin ya ake yiwa saurayi fira?

Amsa dayace, shine ki rika gaya masa kalamai masu dadi.

Idan saurayi yana sonki da gaske, jin muryarki kawai nishadi yake bashi, Dan haka ke kuma sai ki san yanda zaki rika gaya masa kalamai masu dadi, dan kinsan ance in kana da kyau ka kara da wanka.

Bisa al’ada, yawanci saurayine me jan ragamar hira, watau shine zai rika tsokano magana wadda zata sa kema ki buda baki Ku yi ta yi, amma zamani yasa a yanzu ‘yan mata ma na Jan ragamar fira.

Karanta Wannan  Ya ake samun saurayi

Abubuwa da zaki rika yiwa saurayinki hira akansu sune abubuwan dake burgeki, kamar film, waka, karatu, tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ko guraren shakatawa da sauransu.

Kamata yayi ya zama abokinki, dan haka zaki iya bashi labarin kawancenki da kawarki ko kuma alakarki da yayarki da kuma irin kulawar da take baki.

Kina kuma iya bashi labarin wani subject a makaranta da kike jin dadin shi ko kuma wanda yake baki wahala.

Hakanan zaki iya bashi labarin irin yanda kike son rayuwar soyayya da yanda zata kaiku ga aure.

Kuma ki rika magana akan wani abu ko dabi’a tashi dake burgeki, misali, idan me son saka turarene, kina iya gaya masa cewa, kamshin turarensa na debe miki kewa, idan me gemune, kina iya gaya masa yanda gemunsa ke burgeki da irin kular da yake baiwa gemun, idan me ilimine shima ki rika yabonsa ta bangaren.

Karanta Wannan  Saurayina ya yaudareni

Idan takalmi yasa, kina iya cewa, “kai kaga kuwa yanda takalmin nan yayi kyau a kafarka?, kamar ka bani Aron kafar” dadai sauransu.

Idan ke me fitace, ya kamata ki rika bashi labarin abubuwan ban mamaki, na burgewa, ko ban haushi da kuka gani a hanya.

Idan kika ji yana kokarin yi miki jawabi akan wani Abu, ko da kin san abun, kada ki katseshi, ki barshi ya kammala kuma ki Nuna masa jin dadi ko mamakin sanin abinda ya gaya mikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *