Saturday, January 4
Shadow

Hankula sun koma kan Shugaban kamfanin mai na kasa NNPCL yayin da saura kwanaki kalilan ya cika shekarun barin aiki

Shugaban kamfanin mai na kasa, NNPLC, Mele Kolo Kyari, saura kwanaki kalilan ya cika shekarun barin aiki watau 60.

Nan da ranar 8 ga watan Janairu ne dai Mele Kolo Kyari zai cika shekaru 60 wanda a doka ya kamata ya sauka daga kan mukaminsa dan a nada wani shugaban kamfanin.

Mele Kolo Kyari shine shugaban kamfanin NNPCL da yafi dadewa akan kujerar tun bayan da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nadashi mukamin a ranar July 2019 inda a yanzu ya shafe shekaru sama da biyar akan kujerar kenan.

Saidai inda gizo ke sakar shine Bayan da kamfanin NNPC ya koma na ‘yan kasuwa ya fita daga hannun Gwamnati ya kuma canja suna zuwa NNPCL, doka ta baiwa Mele Kolo Kyari damar zai iya ci gaba da zama a matsayin shugaban kamfanin har nan da shekarar 2027.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Magoya Bayan Sarki Sanusi II Sun Yi Wa Gwamna Abba Kyakkyawar Tarya A Hanyarsa Ta Dawowa Daga Filin Jirgi A Safiyar Yau Domin Nuna Farin Cikinsu Da Sake Nadin Sabon Sarkin Kanò

Wasu rahotanni kamar yanda jaridar Punchng ta ruwaito sunce akwai wani me suna Bayo Ojulari da ake tsamanin shine zai maye gurbin Shugaban kamfanin na NNPCL.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *