Saturday, May 17
Shadow

Ban yi wata murna sosai da zama shugaban kasa ba, saboda irin barnar da na iske n yiwa Najeriya>>Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, bai yi wata murna da zama shugaban kasa ba bayan da ya iske irin barnar da aka yiwa Najeriya.

A bayyana hakane ga kakakin majalisar dattijai, Godwill Akpabio.

Akpabio ne ya bayyana hakan a wajan rabon kayan da yayi ga mutanen mazabarsa wanda suka hada da kayan abinci da ababen hawa da sauransu a jiharsa ta Akwa-Ibom.

Yace wata rana ya taba tabayar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan shin ko yayi murnar zama shugaban kasa kuwa lura da irin barnar da ya iske tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele yawa kasar?

Sai shugaba Tinubu yace masa murna kadan yayi. Bai san barnar da akawa Najeriya ta kai haka ba.

Karanta Wannan  Idan da gaske kake game da daina Shigo da abubuwa daga kasashen waje a rika Amfani da wanda aka yi a Najeriya, ka ajiye motocin Alfarma da kake hawa ka koma Amfani da motocin Innoson da ake kerawa a jihar Anambra>>Atiku ya gayawa Tinubu

Akpabio ya kara da cewa, ya gayawa shugaban kasar cewa, yayi imanin kamar yanda ya gyara Legas, Itama Najeriya zai gyarata haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *