Tuesday, January 7
Shadow

Akwai yiwuwar Man United ta koma ƙasan teburi – Amorim

Shekara 50 kenan rabon da Manchester United ta faɗi daga gasar Premier League.

Man United na ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suka zarta kowacce samun nasara a Ingila da ma duniya baki ɗaya, kuma mun saba ganin kulob ɗin yana shiga tsaka mai wuya a lokuta daban-daban.

Sai dai a wannan karon lamarin ya sha bamban. A daren da ya gabata ne Newcastle ta doke Man United 2-0 har gida.

Bayan kammala wasan da Newcastle ɗin ta ɗaiɗaita United a minti 30 na farko, mai horarwa Ruben Amorim ya fara tunanin faɗawa “relegation zone” – wato komawa ƙasan teburi.

Da sashen BBC Sport ya tambaye shi game da ko suna ƙoƙarin guje wa faɗawa ƙasan teburin a yanzu, Amorim ya amsa da cewa: “ina akwai yiwuwar hakan. Dole ne mu faɗa wa magoya bayanmu gaskiya.”

Karanta Wannan  Kalli Kayataccen hoton Nafisa Abdullahi

Sakamakon wasan ya sa United ta koma ta 14 a teburi da tazarar maki bakwai tsakaninta da ‘yan ukun ƙarshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *