Tuesday, January 7
Shadow

Najeriya ta ware biliyan 60 na ciyar da ƴan firamare a 2025

Gwamnatin Najeriya ta ware naira biliyan 60 domin ciyar da ‘yan makarantar firamare a sassa daban-daban na kasar a cikin kasafin kudin 2025.

Za ai aikin ne karkashin shirin gwamnati na farfado da tattalin arziki wato Economic Recovery Growth Plan (ERGP).

Jaraidar Dailty Trust ta tawaito cewa, kafin a sauya ministan ilimin kasar ya fara sanar da hakan wanda dama shirin ciyar da daliban yake karkashin ma’aikatarsa, kafin daga bisani a mayar da shi karkashin ofishin shugaban kasa.

An ware wa ma’aikatar ilimi kudi naira biliyan 348, cikin sama da naira tiriliyan 2. 517, wanda hakan na daga cikin fannin da ya fi samun kaso mai tsoka a kasafin kudin, duk da bai kai adadin da Bankin Duniya ya bayar da shawara na kashi 20 zuwa 30 cikin 100 na kasafin kudin ba.

Karanta Wannan  JARABTA: Cikin Kwanaki Uku A Jere, Ya Rasa Matarsa Da Yaransa Biyu

Har wa yau, ma’aikatar ilimin za ta samu naira biliyan 50, domin tallafa wa shirin mayar da yaran da ke gararanba kan tituna makaranta, akwai wani kudin na daban da za a samar da kayan karatu a makarantun firamare da sakandare a daukacin jihohi 36 na Najeriyar.

Babban birnin tarayya Abuja zai samar da kayan karatu na zamani a kwalejoji 118 a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *