Tuesday, January 7
Shadow

YANZU YANZU: litar Man fetur zata koma Naira (500) nan Nada jimawa Ba, Dangote

Bayan karya farashin litar Man fetur ɗinsa a yan kwanakin nan Dangote ya Sake ƙulla yarjejeniya da kamfanoni biyu don karya farashin man fetur

Kamfanin matatar mai ta Dangote ya bayyana cewa ya ƙulla yarjejeniya da kamfanonin Heyden Petroleum da Ardova Plc don tabbatar da samar da man fetur a farashi mai sauƙi ga ƴan Najeriya.

Cikin wata sanarwa da matatar man ta Dangote ta fitar a jiya Alhamis, ta ce kamfanonin biyu sun shiga yarjejeniya ta sayan mai da yawa daga matatar Dangote, tare da samun tallafi daga shirin sayen ɗanyen mai da Naira da Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar.

“Wannan mataki na dabarun kasuwanci an tsara shi ne don tabbatar da wadatar dangogin mai a farashi mai rahusa, daidaita kasuwar man fetur ta ƙasa, tare da inganta tsaro wajen samar da makamashi ga masu amfani,” inji sanarwar.

Karanta Wannan  Ni da 'yan Najeriya muna cikin farin cikin gyara matatar mai ta Warri - Tinubu

Dangote ya ce wannan ci gaban ya biyo bayan misalin da kamfanin MRS ya kafa, wanda ya riga ya shiga irin wannan yarjejeniya da Dangote .

Sakamakon haka, MRS ya rage farashin mai zuwa Naira 935 kowace lita a duk gidajen manfetur dinsa a faɗin ƙasa, don magance matsalar bambancin farashi tsakanin jihohi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *