Tuesday, January 7
Shadow

Ba zan yi aure yanzu ba saboda idan na yi aure za’a daina yayina>>Rahama Sa’idu

Tauraruwar Tiktok, Rahama Sa’idu ta bayyana cewa ba zata yi aure yanzu ba saboda bata son a daina yayinta.

Ta bayyana hakane a wani faifan bidiyonta da ya watsu sosai a kafafen sadarwa inda a bidiyon aka ganta tana waya a cikin mota.

Ta bayyana cewa, ba zata yi aure ba har sai bayan mulkin Tinubu.

Rahama dai ta bayyana wani gida inda tace saurayinta ne ya siya mata akan Naira miliyan 50 kuma ya saka mata kayan Naira Miliyan 20.

Lamarin ya tayar da kura sosai a kafafen sada zumunta inda akaita bayyana mabanbanta ra’ayoyi akanta.

A kwanakin bayane dai Rahamar ta bayyana mota da wayar iPhone da aka siya mata wanda shima ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.

Karanta Wannan  Mahaifiyar Gwamnan Jihar Jigawa Ta Rasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *