Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta sanar da dakatar da tauraruwa Samha Inuwa saboda zargin yin shiga mai nuna tsiraici.
Shugaban hukumar Abba El-Mustapha shi ya tabbatar wa da BBC hakan, inda ya ce an dakatar da Samha na aƙalla tsawon shekara ɗaya.
“Cikin abubuwan da suka sa muka da dakatar da ita har da furta kalamai marasa kyau waɗanda ba ɗabi’ar ƴan Kannywood bane,” in ji El-Mustapha.
Rahotanni sun ce hukumar ta sha yi wa tauraruwar ta Kannywood gargaɗi kan irin shiga mara kyau da kuma yin kalamai da ba su dace ba a wasu bidiyoyinta, sai dai ta bijire wa hakan kamar yadda hukumar ta yi zargi.