Hukumar karɓar haraji ta jihar Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti da nufin inganta harkokin tsaro.
Hukuma ta ce za a yi hakan ne kuma don ƙara yawan kuɗaɗen shiga da ake samu.
Yanzu dai za a sauya wa motocin haya da keke-NAPEP launi domin a bambance tsakanin ababen hawa na haya da kuma waɗanda ba na haya ba. Launin ja ko tsanwa.
Hon Moses Abeh wanda ya wakilci gwamnatin jihar a taron kaddamar da tsarin, ya ce an ɗauki aniyar yin tsarin ne domin samar da lambobin tsaro da kume fentin ga direbobi domin kare kai daga ɓata-gari da ake kira ‘One Chance’.
“Lambar tsaron zai kunshi bayanan direba da suka haɗa da wajen da mutum ya fito da kuma inda yake zama,” in ji Moses.
Ya kuma ce dole sai an san ƙungiya da direba ke ciki domin kaucewa sajewa da ɓata-gari ke yi a matsayin direbobi.
Ƙungiyoyin direbobi da abin ya shafa sun nuna farin ciki da wannan sabon tsari, inda suka ce hakan zai sa a gano masu aikata laifi.
Sun kuma amince da fenti mai launin ja ko tsanwa wanda suka ce shi ya fi dacewa a saka wa motocin.