Thursday, January 9
Shadow

Ban damu da zagin da ake min ba, gyaran Najeriya ne a gabana>>Shugaba Tinubu

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa yana sane da irin maganganun da ake fadi akansa amma duk basu dameshi ba saboda gyaran Najeriya ne a gabansa.

Ya bayyana hakane yayin ganawa da dattawan yankin Inyamurai na kudu maso gabas a ziyarar aiki da ya kai yankin ranar Asabar.

Shugaban yace yasan irin aikin da ya nema kuma yasan za’ayi ta zaginda da maganganu marasa dadi, yace amma ya toshe kunnensa.

Shugaban yace cire tallafin ma da yayi duk da akwai zafi amma ya zama dole dan a samu kudin gyara kasa, musamman dan manyan gobe su ji dadi.

Karanta Wannan  NAPTIP ta kuɓutar da mutum 285 da aka yi safararsu zuwa Kano a 2024

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *