Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya sallami kwamishinoni 5 daga gwamnatinsa a kokarin yin garambawul da inganta tafiyar da mulki.
Me magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Talata.
Kwamishinonin da aka sauke sune;
Dr. Jamila Dahiru (Education)
Abubakar Bununu (Internal Security and Home Affairs)
Usman Danturaki (Information and Communication)
Prof. Simon Yalams (Agriculture)
Yakubu Hamza (Religious Affairs and Societal Reorientation)
Gwamnan yace ya godewa kwamishinonin bisa gudummawar da suka bayar wajan nasarorin da aka samu a gwamnatinsa.
Sannan ya bayar da sunayen sabbin kwamishinoni 8 ga majalisar jihar dan tantancewa, wadanda aka bayar da sunayen nasu sune kamar haka:
Isa Tilde
Abdullahi Mohammed
Dr Bala Lukshi
Usman Shehu
Iliyasu Gital
Prof. Titus Ketkukah
Adamu Gabarin
Dr Mohammed Lawal.