Friday, May 16
Shadow

Yarabawa miliyan 60 sun shirya ficewa daga Najeriya – Akintoye

Shugaban Ƙungiyar Ƙudirin samar da ‘Yancin Kai ta Yarbawa, Farfesa Banji Akintoye, ya jaddada cewa ƙungiyar ba za ta janye daga neman kafa ƙasar Yarabawa ba.

A cewar Akintoye, kimanin Yarabawa miliyan 60 ciki har da mazauna gida da ‘yan ƙasashen waje, suna goyon bayan ƙudirinsa na kafa ƙasar Yarbawa a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.

Da ya ke tattaunawa da jaridar The PUNCH a jiya Litinin, Akintoye ya ce, “Ba za mu koma baya ba. Dole ne mu fice daga Najeriya, ko kuma ƙasarmu za ta shiga matsala.

“Ba kwa jin muryar mu a tituna? Ƙasar Yarabawa yanzu, babu gudu ba ja da baya.

Karanta Wannan  Dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara na Tangal-Tangal yana ta neman 'yan Majalisa su amince masa domin idan basu amince ba dole ya janye dakatarwar

“Muna nufin Yarabawa da ke Nijeriya, kusan mutane miliyan 55 zuwa 60. Muna so mu kafa ƙasa ta kanmu. Ba za a samu Najeriya ba idan muka kafa ƙasarmu. Amma idan sauran suna son ci gaba da kasancewa a matsayin Najeriya, babu matsala,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *