Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta tsare jami’anta 10 game da zargin hannunsu a ɓacewar wasu kayayyakin aiki.
An kama jami’an ne a makon da ya gabata, kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafukan zumunta ta bayyana yau Laraba.
“Jami’an da aka kama makon da ya gabata bisa umarnin Shugaba Ola Olukoyede, na amsa tambayoyi game da ɓatan wasu kayayyakin aiki,” in ji kakakin EFCC Dele Oyewale.
Wannan sanarwa na zuwa ne bayan hukumar ta sanar da korar jami’an nata 27 a shekarar da ta gabata saboda “zambatar mutane” da sauran laifuka.