Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kwanannan za’a kara kudin kiran waya daga sayen data.
Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Bosun Tijani ne ya bayyana haka.
Ya bayyana hakane a wajan wani taron masu ruwa da tsaki ranar Laraba a Abuja.
Yace kamfanonin sadarwa na neman a basu damar kara farashin kudin kira dana sayen data da kaso 100 bisa 100 amma ba za’a yadda da hakan ba.
Yace za’a yi karin inda za’a kare kowane bangare tsakanin kwastomomi da Kamfanin. Yace ana jiran hukumar NCC ne dan ta fitar da tsarin yadda karin zai kasance.