Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar dakarun ƙasar, da aka kashe a harin da mayaƙan Boko Haram ta kai wani sansanin soji da ke ƙauyen Sabon Gida, cikin ƙaramar hukumar Damboa a jihar Borno.
Cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ƙasar ta fitar, ta ce Tinubu ya jajanta wa rundunar sojin ƙasar sakamakon mutuwar dakarunta shida a harin.
Haka kuma shugaban ƙasar, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya haddasa harin, domin ɗaukar matakan hana faruwar makamancinsa a nan gaba”.
A ranar Asabar ne mayaƙan ISWAP suka ƙaddamar da hari da asuba kan sansanin sojin inda suka yi arangama da sojoji, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin ƙasar shida da mayaƙa fiye da 30.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa sojojin ƙasar bisa jajirewar da suka yi, har ta kai ga sun samu nasarar daƙile harin harin, tare da kashe gomman mayaƙan ƙungiyar.