Rahotanni daga ofishin hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC sun bayyana cewa an nemi tsabar kudi har dala $350,000 zuwa dala $400,000 ba’a gani ba.
Hakanan akwai wasu gwalagwalai na miliyoyin Naira da suma auka bace tare da kudin.
Lamarin ya farune a ofishin hukumar dake jihar Legas, kamar yanda kafar PRNigeria ta ruwaito.
Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da EFCC ta kori ma’aikata 27 saboda samunsu da rashawa da cin hanci da zamba cikin aminci.
Wannan lamari yasa ‘yan Najeriya na diga ayar tambaya akan hukumar ta EFCC da aka sani da yaki da rashawa da cin hanci amma da alamu me dokar bacci na neman bugewa da yin gyangyadi.
Majiyar tamu tace ta yi kokarin jin ta bakin kakakin EFCC kan wannan sabon lamari amma abu ya faskara.