Friday, December 6
Shadow

An kàshè mutum fiye da 1500 da sace fiye da 2000 a Najeriya – NHRC

An kashe mutum fiye da 1500 da sace fiye da 2000 a Najeriya – NHRC.

Hukumar kare haƙƙin bil-adama ta Najeriya, wato NHRC, ta bayyana cewa, tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na wannan shekara, an sami aukuwar sace-sacen jama’a kusan 2000, aka kuma halaka wasu kusan 1500 a sassan kasar.

Jami’an hukumar ne suka bayar da wannan rahoto, a wajen wani taron tuntuɓa na kuniyoyin farar hula, kan halin da ake ciki game da batutuwan da suka shafi al’amuran kare hakkin bil’adama a kasar, wanda hukumar ta shirya tare da hadin gwiwar ƙungiyar tarayyar Turai, kuma aka gudanar yau a babban birnin tarayya Abuja.

Rahoton ya ce an sace mutum 1712 sannan an kashe mutum 1463 a wurare daban-daban na Najeriya, daga watan Janairu zuwa watan Satumba na bana.

Karanta Wannan  Masu fama da kwalara na ƙaruwa a Najeriya

Hukumar kare haƙƙin bil’adaman ta Najeriya ta kuma yi tsokaci, cewa an sami ƙaruwar adadin yara ƙanana da ake yi watsi da su a rariya, inda a cikin watan Satumban da ya gabata aka lissafa aukuwar hakan har sau 2723.

Dangane da kisan jama’a da kan auku a Najeriyar kuwa, hukumar kare haƙƙin bil’adaman ta ƙasar ta danganta hakan da ƙarin ɗibar yara da ta ce ƙungiyoyin ‘yan ta’adda suke yi, kuma suke tafka ta’asa a kasar.

Alkaluman da hukumar kare haƙƙin bil-adaman ta Najeriyar ta gabatar a wajen wancan taro dai sun fayyace ƙamarin munin aukuwar tashe-tashen hankula da keta haƙƙokin bil’adama da ke aukuwa a sassan ƙasar.

Karanta Wannan  Soyayyar Da Nake Yi Wa Tinubu Da Shettima Ta Sa An Je Har Wurin Sana'ata An Sace Min Turaren Da Nake Siyarwa, Don Haka Daga Yau Na Bar Tafiyar Tinubu/Shettima, Inji Bashir Musa Maiturare Daga Garin Nguru, Jihar Yobe

Ƙungiyar dai ta bayyana al’amarin da wani abu da ke ci gaba da zama babban ƙalubale, kuma yana nan yana dakon a shawo kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *