Friday, December 5
Shadow

El-Rufai ne ya sani, Inji tsohon Kwamishina a Gwamnatin Jihr Kaduna Bashir Sa’idu da aka kama sa satar kudi

Tsohon Kwamishina a jihar Kaduna lokacin mulkin tsohon Gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, watau Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu da yanzu haka yake tsare bisa zargin satar kudaden gwamnati, yace Gwamna El-Rufai ne ya sashi duk abinda yayi.

Ya bayyana hakane a cikin jawabin da ya baiwa ‘yansanda bayan kamashi, kamar yanda wani dansanda da baiso a bayyana sunansa ya gayawa manema labarai kamar yanda jaridar TheNation ta ruwaito.

Ana zargin Alhaji Muhammad Bashir Sa’idu da sayar da daloli mallakin jihar ta Kaduna akan farashin da bai kamata ba.

Kotu tace ya aikata laifinne a shekarar 2022.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Rawar da Ali Nuhu ya tika da Rahama Sadau ta sa ana ta cece-kuce inda wasu ke cewa, wai yaushe zai girma?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *