Hukumar alhazan Najeriya, NAHCON ta gargadi maniyyatan kasar kan sayar wa wadanda ke zaune a Saudiyya domin neman kudi da aka fi sani da ‘takari’ tufafin da hukumar ta dinka musu domin gudanar da ayyukan hajjin.
Daraktan Da’awah na hukumar ta NAHCON reshen jihar Kebbi, Sheikh Aminu Hassan ne ya bayyana haka lokacin da yake yi wa maniyyatan jhar jawabi bayan isarsu kasa mai tsarki.
Akwai zarge-zargen cewa takarin na sayen tufafin wasu maniyyatan musamman mata da kudi masu yawan gaske, tare da yin bad da bami domin shiga cikinsu da fakewa da aikin hajjin wajen aikata abubuwan da ba su dace ba.
Sheikh Aminu Hassan ya ce sayar da tufafin babban laifi ne da zai iya janyo wa duk wanda ya aikata hukunci mai tsanani, don haka ne ya gargadi maniyyatan su kauce wa wannan mummunar dabi’a.
“Hakika za ka iya samun kudi masu yawa a wajen takarin, musamman ku mata, to amma ku tuna cewa za su yi amfani da tufafin ne wajen aikata barna, sannan ku sani cewa za a danganta barnar da Najeriya da ma jihar Kebbi musamman”, in ji shi.
Daraktan ya kara da cewa ”ku tuna cewa tufafinku alama ce ta kasa da jihar da kuka fito, don haka ku kiyaye duk wani abu da zai bata wa kasarku suna”.
Sheikh Aminu Hassan ya kuma yi kira ga maniyyatan su kauce wa yawan kashe kudade babu gaira babu dalili sannan su lura sosai wajen yin canji domin kauce wa fadawa hannun mazambata lokacin gudanar da aikin hajin na bana.